A wani taron koli da aka yi a Brussels, babban birnin Belgium, kungiyar ta tarayyar turai ta samarwa da Turkiyya da agajin kudi na dala biliyan 3.2, domin ta lura da miliyoyin ‘yan gudun hijrar da ke zaune a kasar ta Turkiyya.
Babbar tawagar ‘yan gudun hijra daga Syria wadanda suka isa nahiyar Turai a wannan shekara sun ratsa ta Turkiyya, yayin da su ke kan hanyarsu ta zuwa Girka da Bulgaria.
Shugaban kwamitin kungiyar ta tarayyar turai Donald Tusk, ya fada a taron manema labarai na hadin gwiwa da suka gabatar tare da Firai ministan Turkiyya, Ahmet Davutoglu da shugaban kwamitin zartaswar kungiyar kasashen turai Jean-Claude Juncker cewa, matsayar da aka cimma, ta tsara yadda za a samar da daidaito a iyakokin kasashen nahiyar.
Tusk ya kara da cewa za a kara assasa batun yunkurin da Turkiyyan ke yi na samun gindin zama a kungiyar kasashen turan.
A shekarar 1997 aka ayyana Turkiyya a matsayin kasar da ta cancanci ta shiga kungiyar, inda tuni ta fara shirye-shiryen samun gurbi na dindindin a shekarar 2005 a hukumance.