Fitaccen Malamin addinin Musulunci, Dr. Ahmad Mahmud Gumi ya ce tun da an sami sauyin gwamnatin tarayya to wajibi ne a yi mata tayin sulhu da 'yan bindiga don magance matsalar tsaron da ta addabi Arewacin Najeriya.
Dama a can baya lokacin tsohon shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Sheikh Ahmed Mahmud Gumi ya sha yiwa gwamnatin tayin sulhu da 'yan bindiga amma bai sami karbuwa ba, kuma ya ce tunda manyan kasa sun sake ta da maganar, wajibi ne a jawo hankalin sabuwar gwamnatin Bola Ahmed Tinubu.
Dr. Gumi ya ce sulhu ba ya nufin gazawar jami'an tsaro a Najeriya amma hanya ce ta magance matsalar tsaro cikin sauki. Ya ce tun da sabuwar gwamnati aka samu to maganar sulhun kan iya yin tasiri.
Duk da hangen sararin samun sauki da wasu ke yi idan aka yi sulhu da 'yan-bindiga, masana harkokin tsaro irin su Manjo Yahaya Shinko mai ritaya na ganin akwai wasu abubuwan dubawa.
Da yawan mutane na ganin zai yi wuya ma 'yan-bindigar su kara kulla sulhu da gwamnati ganin irin abubuwan da su ka faru a baya, sai dai kuma Dr. Ahmad Gumi ya ce babu matsala idan har za'a yi da gaske.
Jihohin Kaduna, Zamfara, Niger, Filato, Katsina da Sokoto ne su suka fi fama da hare-haren 'yan-bindiga, kuma wasu na ganin tunda hare-haren 'yan bindigar ya ki ci ya ki- cinyewa, to sulhu ne kawai mafita.
Saurari rahoton a sauti:
Dandalin Mu Tattauna