abuja, nigeria —
Biyo bayan jerin dimbin takunkuman da ECOWAS ta kakaba wa jamhuriyar NIJAR bayan da sojojin da ke tsaron fadar shugaban kasa su ka hambarar da zababbiyar gwamnatin farar hula ta Bazoum Mohammed, wannan ya ja hankalin masana.
DR. Umar Ardo da ke zama kwararre kan sha'anin tsarokuma tsohon malami a makarantar horas da hafsoshin sojojin Najeriya wato NDA na ganin matakan sun yi tsauri da yawa.
DR Ardo wanda ya ce shi ma sam bai yarda da juyin mulki ba, to amma lalle akwai bukatar a kai zuciya nesa kana ayi takatsantsan sannan abi wannan maganar ta diflomasiyya.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna