washington dc —
Kungiyar ECOWAS ta gudanar da wani taron manema labaru a sakatariyarta da ke Abuja babban birnin Tarayyar Najeriya inda ta yi karin haske tare da fayyace matsayinta kan irin matakai masu zafi da take daukawa akan sojojin da su ka yi juyin mulki a jamhuriyar Nijar.
Taron manema labarun, wanda shugaban hukumar gudanarwar ECOWAS SIR Omar Aliyu Moussa ya jagoranta, ya yi bayanin cewa ECOWAS ba wai tana so ko tana daura damarar yaki da mutanen Jamhuriyar Nijar ba ne, amma dai babban burinta shi ne ganin an maido da tsarin doka a kasar.
Saurari shirin:
Dandalin Mu Tattauna