Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsohon shugaban kasar Najeriya Umar Musa Yar'aduwa ya cika shekaru 13 da rasuwa.


Tsohon Shugaban Najeriya Umar Musa ‘Yaraduwa
Tsohon Shugaban Najeriya Umar Musa ‘Yaraduwa

An haifi shugaba Yar'adua ne a ranar 16 ga watan Agustan shekarar 1951 a jihar Katsina ta Najeriya.

Shi ne shugaban kasa na farko da aka zaba a karkashin jam’iyyar PDP bayan dawowar mulkin damokaradiyya a Nijeriya a shekarar 1999.

Shugabancin sa ya kasance ne da jajircewarsa wajen bin doka da oda, yaki da cin hanci da rashawa, tare da jaddada muhimmancin, ilimi da noma.

Sai dai yayi fama da jinya a tsawon , Shugabancin nasa , da a karshe ya yi sanadiyyar rasuwarsa a ranar 5 ga watan Mayun 2010, yana da shekaru 58.

Bayan rasuwar sa, an rantsar da Mataimakin shugaban kasa na lokacin, Goodluck Jonathan, a matsayin sabon shugaban kasa.

Tsohon Shugaban Najeriya Umar Musa ‘Yaraduwa
Tsohon Shugaban Najeriya Umar Musa ‘Yaraduwa

A duk lokacin tunawa da Marigayi Yar'adua, mutane da dama suna yabawa da jajircewarsa wajen bin doka da oda da kuma kokarin da ya yi na yaki da cin hanci da rashawa a lokacin da yake kan mulki.

Wasu kuma sun bayyana yadda ya mayar da hankali kan ilimi da noma, da kuma tasirin da manufofinsa suka yi a kan wadannan bangarorin.

Duk da ya ke bai dade a kan karagar mulki ba, tsohon Shugaban kasar ya yi matukar tasiri a rayuwar al'umma da kuma damokaradiya a Najeriya.

A yayin da al’ummar kasar ke tunawa da kuma jinjina wa Shugaba ‘Yardua, iyalansa da masoyansa na ci gaba da nuna alhinin rashinsa.

XS
SM
MD
LG