Obasanjo wanda ya yi jawabin daga dakin karatun sa a Otta jihar Ogun, ya yi ikirarin cewa shugaba Buhari ya yaudari ‘yan Najeriya a ka zabe shi a karo na farko, don haka ba daidai ba ne ‘yan Najeriya su sake ba da irin wannan dama.
A cikin wasika da ya rubuta ya kafa hujja da bayanan sakataren tsohuwar jam’iyyar shugaba Buhari, wato CPC Injiniya Buba Galadima ya ce Buharin ba ya daukar shawara.
Muryar Amurka ta tuntubi Buba Galadima don jin martanin sa kan wannan batun, inda ya tabbatar da cewa hakan gaskiya ne.
Kazalika Obasanjo ya yi magana kan zargin hukumar zabe ba ta da niyyar yin zaben adalci ko kuma shugaba Buhari na son dawowa mulki ko ta halin kaka.
A bayaninsa kan batun, Buba Galadima ya yi a matsayin sa na kakakin kamfen na babbar jam’iyyar adawa ta PDP, ya ce rashin sanya hannu kan dokar zabe da neman gurfanar da bababn alkali Walter Onnoghen gaban kotu shaidu ne na rashin adalcin.
Yanzu dai ya rage kasa da wata daya a gudanar da babban zaben a ranar 16 ga watan gobe.
Domin cikakken bayani saurari rahotan Saleh Shehu Ashaka.
Facebook Forum