Cikin shekarun 1990, aka sace wa Najeriya wadannan kudaden karkashin mulkin tsohon shugaban kasa na soji, Janar Sani Abacha, aka kuma boye su a kasashen waje. Yanzu sama da shekaru 20, ana shirin mayar wa ‘yan Najeriya wadannan kudade.
Karkashin yarjejeniyar da aka cimma gwamnatin Najeriya za ta yi amfani da kudaden a wasu fannoni uku masu muhimmanci ga farfado da tattalin arziki a fadin kasar. Domin tabbatar da an yi amfani da kudaden ta hanyar da ta kamata don ci gaban al’umma, yarjejeniyar ta samar da hanyoyin da za a saka ido.
Haka kuma, Najeriya za ta biya duk wasu kudade da suka salwanta sanadiyar cin hanci ko damfara.
Wannan jarjejeniya dai wata alama ce ga shirin da Amurka ta samar kan yaki da cin hanci da rashawa. Haka zalika ta yaba wa kudurin gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, kan yaki da cin hanci da rashawa.
Cikin tawagar gwamnatin Najeriya da suka zo Amurka don kulla yarjejeniyar akwai ministan Shari’a Abubakar Malami, wanda ya ziyarci sashen Hausa na Muryar Amurka. Ministan ya tabbatar da cewa tsohon shugaban ya kwashi makudan kudade daga lalitar gwamnatin kasar.
A tattaunawar su da abokin aikinmu Yusuf Aliyu Harande, Abubakar Malami ya ce wannan batu shine makasudin zuwan su, kuma kasashen biyu sun amince kudaden za su baro tsibirin Jersey nan da kwanaki 28 su iso Amurka sannan su isa Najeriya cikin kwanaki 43.
Malami, ya ce wadannan kudade a zamanin mulkin soja, karkashin gwamnatin Marigayi Abacha a aka fitar da su a matsayin sunayen kamfanoni da wasu mutane.
Da ya ke mayar da martani, tsohon babban jami’in tsaron marigayi Janar Abacha, Majo Hamza Al-Mustapha, ya ce ya fadawa gwamnatocin baya cewa su fara bincikar sa tukun, idan an ga ya saci kudi a hukunta shi kada a tausaya masa.
Ya ce shekaru 22 da rasuwar Janar Sani Abacha, amma kullun zancen kudade ake kamar basa karewa.
Haka kuma, ya bayyana matakan da gwamnatin Abacha ta dauka lokacin da Amurka take yunkurin kakaba mata takunkumi, wanda ya saka gwamnati ta dau matakan ajiye kudade a waje na kar-ta kwana.
Majo Almustapha ya kalubalanci gwamnati cewa, bayan rasuwar Abacha ina wandannan kudaden suke?
Ya ce shi dai a iya sannin sa a shekara hudu da wata bakwai da Abacha ya yi yana mulki basu je Amurka ba, saboda haka wane ne ya je ya ajiye wadannan kudade da ake Magana akai?
Domin cikakken bayani saurari tattaunawa da Abubakar Malami da Hamza Al-Mustpha:
Facebook Forum