Majalisar Dokokin Jihar Zamfara ta bai wa sakatariyarta iznin ta rubuta wasika zuwa Ministan tsaro, Mansur Dan Ali, kan yadda hare-hare ke salwantar da dumbin rayukan jama'a a yankin.
Jaridar Punch wacce ta ruwaito labarin ta bayyana cewa, majalisar ta yanke hukuncin ne a zaman da ta yi jiya Juma’a.
Daukan wannan mataki na zuwa ne bayan da dan majalisa mai wakiltar mazabar Maru ta Kudu, Alhaji Abdullahi Dansadau, ya gabatar da korafi a gaban majalisar a wani zangon zaman majalisar da ke sauraren bukatu na gaggawa.
Dansadau ya bayyanawa majalisar cewa babban abin damuwa ne ganin yadda mutanen da ba su ji ba su gani ba, suke rasa rayukansu a kullum.
‘Yan majalisar wadanda daukacinsu suka amince da a rubuta wasikar sun kuma amince da a nemi karin dakaru a jihar domin su kare aukuwar ire-iren wadannan hare-hare.
Yankin jihar ta Zamfara a ‘yan watannin nan, na fama da mahara da ke far ma kauyuka su kashe dumbin jama’a su kuma kwashi dukiyoyi.
Rahotanni sun yi nuni da cewa a farkon watan nan kadai, an kai wani hari a yankin karamar hukumar Maru, inda ‘yan bindiga suka halaka akalla mutane 30 kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito a shafinta.
Facebook Forum