Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Bada Sanarwar Tarwatsa Tungar Masu Kisa Da Makami A Wasu Jihohi


 Babban Hafsan Sojin Najeriya, Tukur Buratai
Babban Hafsan Sojin Najeriya, Tukur Buratai

Yayinda sojojin Najeriya ke ikirarin tarwatsa tungar wasu masu kisa da makami tare da cafke wasu a jihohin Nasarawa da Binuwai al'ummar yankin Wukari a jihar Taraba kokawa suka yi suna zargin sojojin da laifin kai masu hari

Rundunan sojin kasar a wata sanarwa da ta fitar , ta bayyana cewa ta samu nasarar tarwatsa tungar yan ina da kisa baya ga cafke wasu makiyaya dauke da makamai a jihohin Nasarawa, Binuwai da kuma jihar Taraba bisa zargin cewa suna shirin Kai hari .

To sai dai kuma, yayin da rundunar ke wannan ikirarin, wasu al'ummomi a yankin Wukari na jihar Taraba kokawa suka yi da harin da suke zargin sojoji sun kai musu da sunan yaki da bata gari.

Al'umman Chinkai sun yi zargin cewa an kai musu hari ba tare da wani dalili ba.

Duk kokarin da wakilin sashen Hausa Ibrahim Abdulaziz ya yi, na ji daga bakin daraktan yada labaran rundunan soji a Najeriya Birgediya Janar Texas Chukwu, ya ci tura. An buga wayarsa to amma ba'a dauka ba, haka nan babu amsar sakon kar ta kwanan da aka aike masa.

To sai dai kuma shugaban karamar hukumar Wukari Hon Adi Daniel Adigrace ya bayyana abun da ya sani, a matsayinsa na babban jami'in tsaron yakin inda yace sojojin sun kai hari ne a mabuyan wasu yan ina da kisa na makiyaya.

Sojin sun yi bata kashi da makiyayan wadanda suka kona motocin sojoji biyu tare da haddasa rasuwar soji daya. Sauran sojojin ta kare suka yi kafin a kawo masu doki. Baicin sojan da ya mutu rikicin ya rutsa da ran wani farar hula kana wani kuma ya jikata.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG