Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsaro: Matawalle Ya Nemi Hadin Kan Gwamnonin Arewacin Najeriya


A daidai lokacin da matsalolin tsaro ke kara ta’azzara, gwamna Bello Matawalle na Jihar Zamfara ya yi kira ga sauran takwarorinsa na arewacin Najeriya da ma gwamnatin tarayyar su hada gwiwa wajen samo mafita mai dorewa.

Gwamna Bello Matawalle na jihar Zamfara ya bayyana muhimmancin daukan matakan bai-daya tsakanin gwamnatocin jihohin arewacin Najeriya da hadin gwiwar gwamnatin tarayya domin magance matasalolin tsaro da suka ki ci suka ki cinyewa a yankin.

Bello Matawalle wanda ya tabo batutuwa daban-daban ya kuma bukaci shugabannin arewa su mayar da hankali kan ababen da suke damun al’umma a maimakon siyasa kawai.

Har yanzu dai gwamna Nasiru El-Rufai na jihar Kaduna na ci gaba da jaddada matsayinsa na rashin amincewa da yin sulhu da ‘yan bindigan da ke ci gaba da addabar al’umman yankin arewa maso yamma a Najeriya.

Yanzu dai ‘yan kasa zasu zura ido su ga yadda masu ruwa da tsaki za suyi da shawarar ta gwamna Matawalle.

Saurari rahoto cikin sauti daga Halima Abdulrauf:

Tsaro: Matawalle Ya Nemi Hadin Kan Gwamnonin Arewacin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00


XS
SM
MD
LG