Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dakarun Najeriya Sun Yi Nasarar Dakile Wani Hari A Jihar Borno


Majalisa Ta Tabbatar Da Tsofaffin Hafsoshin Soji A Matsayin Jakadu.
Majalisa Ta Tabbatar Da Tsofaffin Hafsoshin Soji A Matsayin Jakadu.

Rundunar sojin Najeriya ta bayyana cewa dakarun ko-ta-kwanan ta na runduna ta 25 sun sami nasarar dakile wani harin da aka yi yunkurin kaiwa a garin Damboa dake jihar Borno a safiyar Litinin.

Labarin yunkurin kai hari garin Damboa dake da nisan kimanin kilomita 87 da birnin Maiduguri fadar jihar Borno, na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar sojin kasar, Onyema Nwachukwu, ya fitar a yau Litinin.

Haka kuma, rundunar sojin ta bayyana cewa, yan ta’addan sun shigo Garin Damboa ne da kafa da kuma wasu kan babura, amma sojoji suka yi musu barin wuta har suka tsere daga garin kamar yadda gidan Channels ya ruwaito.

Saidai harin ya yi sanadiyyar konewar wasu motoci biyu na rundunar hadin gwiwa tsakanin soji da fararen hula kurmus kuma rundunar soji ta ce tana kan aikin farauto 'yan ta'adda da suka tsere.

A halin da ake ciki yanzu dai, Najeriya na fama da kalubalen tsaro ta fuskoki da dama, wadanda suka hada da yan ta’addan Boko Haram da ke ci gaba da tayar da kayar baya a yankunan Arewa maso gabas, da 'yan bindiga dadi a yankin Arewa maso yamma, yan awaren IPOB da ke tayar da zaune tsaye a yankin kudu maso gabas da kuma rikicin manoma da makiyaya a yankin arewa maso tsakiya da wasu jihohin kudu maso yamma da dai sauransu.

A lokuta da dama gwamnatin Najeriya dai na bayyana kokarin da ta ke yi wajen shawo kan matsalolin tsaro a kasar wanda wasu yan kasar ke cewa ba sa gani a kasa, duba da yadda yan bindiga ke addabar mutane a jihohin Kaduna, Katsina, Zamfara, Neja da dai sauransu.

XS
SM
MD
LG