Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tsaro: Buhari Ya Gana Da Gwamnan Anambra Willie Obiano


Buhari a dama da gwamnan Anambra Willie Obiano a hagu (Facebook/Fadar shugaban kasa)
Buhari a dama da gwamnan Anambra Willie Obiano a hagu (Facebook/Fadar shugaban kasa)

Hukumar zabe ta INEC ta nuna damuwa kan rashin cikakken tsaro a yankin yayin da take shirin tura ma’aikatan da za su gudanar da zaben.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya karbi bakuncin gwamnan jihar Anambra Willie Obiano da safiyar ranar Alhamis.

Ziyarar Obiano a fadar shugaban kasar na zuwa ne kwana guda bayan da rahotanni suka ruwaito cewa mai yiwuwa gwamnatin ta Buhari ta ayyana dokar ta-baci a jihar ta Anambra mai fama da rigingimun masu fafutukar kafa kasar Biafra.

Minisitan Shari’a Abubakar Malami ya fadawa manema labarai a ranar Laraba cewa daga cikin matakan da za su iya dauka wajen kawo karshen tahse-tashen hankula akwai saka dokar ta-baci.

Jihar ta Anambra wacce ke kudu maso gabashin Najeriya na shirin gudanar da zaben gwamna a ranar 6 ga watan Nuwamba.

Hukumar zabe ta INEC ta nuna damuwa kan rashin cikakken tsaro a yankin yayin da take shirin tura ma’aikatan da za su gudanar da zaben.

Jihar ta Anambra ta kwashe watanni da dama tana fama da hare-hare akan ma’aikatun gwamnati da kisan fararen hula da ake dangantawa da masu ‘yan kuniyar IPOB, wadanda a wasu lokuta suke nesanta kansu da hare-haren.

A farkon makon wasu ‘yan bindiga suka kashe Dr. Chike Akunyili miji ga tsohuwar shugabar hukumar NAFDAC marigayiya Dr. Dora Akunyili.

An dora alhakin kisan akan kungiyar ta IPOB wacce ta musanta zargin.

XS
SM
MD
LG