Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Trump Ya Ce Zai Sake Tsayawa Takara A Zaben 2024


Election 2020 Trump
Election 2020 Trump

A daren jiya tsohon shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana aniyarsa ta sake shiga takarar shugaban kasa a shekarar 2024, mako guda bayan da jami’iyarsa ta rage karfi a majalisar dokokin kasar a zaben rabin wa’adi da aka gudanar a makon jiya.

Raunin da Republican ke yi a majalisar dokokin yasa jami’iyar tana nazari a kan ko zata sake tsayar da Trump da yaki amincewa da shan kaye a zaben shekarar 2020, lamarin da ya tada bore kana ya jefa dimokaradiyar Amurka cikin rudani.

“A kokarin sake farfado da martabar Amurka, A wannan dare ina sanar da aniya ta ta shiga takarar shugabancin Amurka,” Trump yana fadawa taron daruruwan magoya bayansa a wani zauren taro a gidansa na Mar-a-Largo, inda yake tsaye da tutocin Amurka kewaye da shi, da allo mai rubutun taken “Sake Maido da darajar Amurka”.

“Farfadowar Amurka tana farawa ne daga yanzu,” yana fada a hukumance yakin neman zabensa na neman gurbin zama dan takara a jami’iyarsa

Sake shiga takarar babban al’amari ne ga kowane tsohon shugaba, musamman wanda ya kafa tarihi a matsayin shugaban kasar da aka taba tsige shi sau biyu, wanda wa’adin shugabancinsa ya kare yayin wani mummunan rikici da magoya baya suka yi a majalisar dokokin kasar domin hana mika mulki cikin ruwan sanyi a ranar 6 ga watan Janairun shekarar 2021.

Trump ya shiga takarar ne a lokacin da jami’aiyarsa ke fuskantar kalubalen siyasa. Ya yi hasashen kaddamar da yakin neman zabensa ne idan jami’iyarsa ta samu gagarumin rinjayi a majalisar dokoki a zaben rabin wa’adi saboda ‘yan takara da ya bawa goyon baya a zaben fidda gwani a wannan shekara. Galibin wadanda ya marawa bayan basu yi nasara ba, lamarin da ya baiwa ‘yan Democrat a majalisar dattawa damar rike kujerunsu kana zasu samun dan rinjayi a majalisar wakilai.

An zargi Trump kan wannan shan kaye da yawancin ‘yan jami’iyar su ka yi, ciki har da karuwan masu cewa sakamakon na nuna lokaci ya yi da ‘yan majalisar dokokin za su manta da shi su nemi mafita ga jami’iyar, inda mutane da dama suka gwammace gwamnan Florida Ron DeSantis da ya yi nasara a zaben makon jiya ya zama dan takarar shugaban kasa a Republican.

XS
SM
MD
LG