Gwamnatin Saudiyya ta yi alkawarin tallafa wa Najeriya wajen gyara matatun manta da ba sa aiki.
Ministan yada labarai Mohammed Idris ne ya bayyan hakan a cewar rahotanni.
Saudiyan ta yi wannan alkawari ne yayin wata ganawa da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya yi da Yarima Mohammed bin Salman a gefen taron koli da Saudiyya ta shirya da kasashen nahiyar Afirka.
“Saudiyya ta yi alkawari za ta saka hannun jari wajen farfado da matatun man Najeriya tare da ba da tallafin kudade don taimaka wa fannin hadahadar kudaden ketare.” In ji Idris.
Najeriya wacce ita ce kasar da ta fi yawan arzikin mai a nahiyar Afirka na shigo da manta daga kasashen ketare saboda matatun manta uku ba sa aiki.
A bara aka kaddamar da matatar man fetur ta Dangote, amma har yanzu ba ta fara aiki ba.
Dandalin Mu Tattauna