Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Sake Neman Tsawaita Wa’adin Dokar Kasafin Kudi Ta 2023


A yau Alhamis aka bayyana hakan, a yayin da Shugaban Majalisar Dattawan, Godswill Akpabio ya jagoranci zamanta bayan dawowa daga hutu domin cigaba da sabon zango a ayyukan majalisar.

Shugaban Kasa Bola Tinubu ya bukaci Majalisar Dattawa ta kara tsawaita wa’adin aiwatar da bangaren manyan ayyuka na kasafin Naira tiriliyan 21 da biliyan 830 na shekarar 2023, da Naira tiriliyan 2 da biliyan 170 na karamin kasafin kudi daga ranar 30 ga watan yunin da muke ciki zuwa 31 ga watan disamba mai zuwa.

A watan Disambar bara ne, dukkanin zaururkan majalisar guda 2 suka tsawaita wa’adin aiwatar da bangaren manyan ayyuka na kasafin kudin na shekarar data soma daga ranar 31 ga watan Disambar zuwa ga ranar 31 ga watan Maris din 2023.

Har ila yau, Shugaban Kasar ya kara neman karin wa’adin aiwatar da kasafin daga 31 ga watan Maris din daya gabata zuwa 30 ga watan Yunin da muke ciki.

Shugaban Majalisar Dattawan yace babban kwamitin majalisar zai tattauna akan bukatar, bayan dawowa daga wani zaman sirri.

Haka kuma, Majalisar Dattawan tayi shiru na minti guda domin girmama marigayi Mataimakin Shugaban Hukumar Kwastam, Etop Essien, wanda ya mutu a Talatar data gabata a cikin ginin majalisar tarayyar, yayin da yake amsa tambayoyi daga mambobin kwamitin majalisar akan asusun ajiyar gwamnati.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG