Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Ya Nada Femi Gbajabiamila A Matsayin Shugaban Ma'aikatan Fadarsa


Shugbaan Najeriya Bola Tinubu Da Shugaban Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila
Shugbaan Najeriya Bola Tinubu Da Shugaban Majalisar Wakilai Femi Gbajabiamila

Shugaban Najeriya Bola Ahemd Tinubu ya sanar da nada kakakin Majalisar Wakilan kasar Femi Gbajabiamila a matsayin shugaban ma’aikatan fadar Shugaban Kasa.

Shugaban kasar kuma ya nada tsohon mataimakin gwamnan jihar Jigawa, Sanata Ibrahim Hassan Hadejia, a matsayin mataimakin shugaban ma’aikatan fadar.

Wadannan nade-nade sun fito ne a cikin wata sanarwa da daraktan yada labarai na fadar gwamnati Abiodun Oladunjoye ya fitar a ranar Juma’a a Abuja.

A wata ganawa da kungiyar gwamnonin jam’iyyar APC wato Progressive Govenors Forum (PGF), shugaban kasar ya kuma nada tsohon gwamnan jihar Benue kuma tsohon ministan ayyuka na musamman a gwamnatin da ta shude, George Akume, a matsayin sakataren gwamnatin tarayya (SGF).

Wannan dai su ne nade-nade na farko da shugaban kasar ya yi tun bayan shan rantsuwar kama aiki a ranar Litinin 29 ga watan Mayu.

XS
SM
MD
LG