Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tinubu Na Neman Ya Ranto N1.77 Trn Daga Ketare


Shugaban Najeriya Bola Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Tinubu

Matukar aka amince, za’a yi amfani da rancen wajen cike gibin Naira tiriliyan 9.7 dake cikin kasafin kudin na bana.

Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya aikewa Majalisar Dokokin kasar, da wasikar neman sahalewa ya ranto bashin Naira tiriliyan 1.77 a matsayin sabon tsarin rancen aiwatar da dokar kasafin kudin bana.

Matukar aka amince, za a yi amfani da rancen wajen cike gibin Naira tiriliyan 9.7 dake cikin kasafin kudin na bana.

Kakakin Majalisar Wakilai ne ya karanta bukatar shugaban kasar a yayin zamanta na yau Talata.

Haka kuma, Shugaba Tinubun ya aike da matsakaicin kasafin da za’a kashe tsakanin 2025 da 2027 ga majalisar tare da kudirin neman yin garambawul ga shirin tallafawa al’ummar kasar, da nufin mayar da kudin bayanan ‘yan kasa ya zama abinda gwamnatin tarayya zata rika amfani da shi wajen aiwatar da shirye-shiryenta na bada tallafi.

Hakan na zuwa ne bayan da a baya-bayan nan babban bankin Najeriya ya bayyana cewar gwamnatin kasar ta kashe dala bilyan 3.58 wajen biyan basussukan da ake binta a ketare a watanni 9 na farkon shekarar 2024 da muke ciki.

Dandalin Mu Tattauna

Tambayoyin wasu ‘yan kasashen Afirka akan manufifi da Shugabancin Donald Trump ga kasashensu
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:10 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG