Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kudin Shigar Gwamnatin Najeriya Ya Karu Da Kaso 76% Zuwa N12.5trn


Nigeria Floating Naira
Nigeria Floating Naira

An danganta wannan katafaren ci gaban da aka samu galibi ga karuwar yawan danyen man da ake fitarwa, wanda ya karu daga ganga miliyan 1.131 a 2022 zuwa ganga miliyan 1.41 a kowace rana a 2023.

Karuwar haraji da kudaden shiga daga cinikin danyen man fetur da gwamnatin tarayyar Najeriya ta samu sun bunkasa abinda ke shiga lalitarta da kaso 76 cikin 100, daga Naira tiriliyan 7.1 a 2022 zuwa Naira tiriliyan 12.5 a 2023.

Sabbin bayanan da aka saki a rahoton matsakaicin kasafin kudin da za’a kashe tsakanin 2025-2027, da tashar talabijin ta Channels ta samu daga ma’aikatar kasafi da tsare-tsaren tattalin arziki, ne suka bayyana wannan cigaba.

A cewar ofishin kasafi, a yayin da jumlar kudaden shiga ta karu da kaso 76 cikin 100, harajin da ake samu daga cinikin danyen mai ya karu da kaso 200 cikin 100 daga tiriliyan N0.8 a 2022 zuwa tiriliyan N2.4 a 2024, inda ya samar da kaso 19.2 cikin 100 na jumlar kudaden shigar da aka samu.

An danganta wannan katafaren ci gaban da aka samu galibi ga karuwar yawan danyen man da ake fitarwa, wanda ya karu daga ganga miliyan 1.131 a 2022 zuwa ganga miliyan 1.41 a kowace rana a 2023.

Harajin da bashi da nasaba da man fetur kuma ya karu da kaso 57.8 cikin 100 daga Naira tiriliyan 6.4 a 2022 zuwa Naira tiriliyan 10.1 a 2023, inda ya bada gudunmowar kaso 80.8 cikin 100 ga jumlar kudaden shigar da aka samu.

A shekarar 2023, an samu jumlar kudin shigar daya kai Naira tiriliyan 7.67, idan aka kwatanta da Naira tiriliyan 9.38 din da aka yi hasashe, abin da ke wakiltar kaso 83.9 cikin 100 na yadda aka aiwatar da kasafin.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG