A cikin 'yan makonnin nan dai kasashen Benin da Nijar su ka ci gaba da kara zarge-zargen na safarar kayayyaki, duk da cewa kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka a watan Fabrairun da ya gabata ta dage takunkumin da ta kakaba wa shugabannin sojin Nijar.
Dangantaka a kan iyakar kuma tana da sarkakiya sakamakon bullar aika-aikan mayakan IS a Nijar da Burkina Faso da ke kara yin barazana ga Benin da makwabciyarta Guinea, Ghana da Togo.
Tun farko kasar Benin ta sanar da bude kan iyakarta a daidai lokacin da kungiyar ECOWAS ta dage takunkumin.
Sai dai iyakar ta ci gaba da kasancewa a rufe a bangaren Nijar, lamarin da ya harzuka shugaban kasar Benin Patrice Talon, wanda ya ce Nijar ta dauke su ne tamkar a matsayin makiyi.
A cewar wani jami’in sojan kasar Benin a Malanville, dan sanda da ke aiki a yankin da kuma mazauna yankin da suka zanta da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP, gadar Malanville da ke samar da mashigar kan iyaka tsakanin kasashen biyu na zaune a rufe a bangaren Nijar, kuma har ila yau, an haramta jigilar kayayyaki a kogin Nijar.
Wasu mazauna Malanville da dama sun shaidawa kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP cewa sojojin Nijar sun tarwatsa su a daya bangaren don haka ba za su iya tsallake kogin ba.
Rufe zirga-zirgar kogin shi ne na baya-bayan nan a jerin shawarwarin da suka shafi kasuwanci tsakanin kasashen biyu.
Dandalin Mu Tattauna