Theresa May itace shugabar wata kasa ta farko da ta gana da Trump a Washington tun da ya dare kan ragamar mulki.
Dukansu biyun sun dauki matakan yiwa dangantakar su da wasu kasashe kwaskwarima musamman akan harkokin kasuwanci.Shirin ficewar Birtaniya daga kungiyar tarayyar turai da kuma fitar da Amirka daga kungiyar kasuwanci kasashen 12 ta Pacific da shugaba Trump yayi, ya zama wajibi suyi shawarwari kula sabbin yarjejeniyoyin harkokin kasuwanci a fadin duniya baki daya.
Tsarin da Teresa May take dashi na fitar da kasar ta daga kungiyar tarayyar Turai ya hada da bada muhimmanci akan iko kan shige da ficen baki, duk da dai har yanzu bata bayyana hakikanin tsarin dokar ba.