Tawagar ‘yan majalisar wakilan na Amurka wacce ke karkashin jagorancin Karen Bass, ta fara ne da ganawa da shugaban kasar Nijar Issouhou Mahamadou, da kuma makardaban gwamnatinsa.
Ziyarar wacce ke gudana a dai dai lokacin da kasar Amurka da jamhuriyar Nijar ke addu’oin tunawa da sojojin da suka rasa rayukansu, sakamakon harin ta’addanci a kauyen Tongo Tongo, na kan iyakar Nijar, da Mali, ta kasance wani lokaci na jajantawa juna wannan babbar asara a tsakanin hukumomin kolin Nijar da tawagar ‘yan majalisar wakilan Amurka.
‘Yar majalisa Karen Bass tace babban dalilin wannan ziyara shine su tantance zahirin yanayin huldar dake tsakanin Amurka, da Nijar, musamman fannin tsaro. Tace sun zo ne da nufin duba ainihin abubuwan dake faruwa a zahiri, da kuma gano ainahin dalilan da ke ingiza mutane rungumar aiyukan ta’addanci, domin samun hanyoyin riga kafin al’amarin.
Da yake ganawa da wadanan wakilan shugaban kasar Nijar Issouhou Mahamadou ya bayyana cewa, dadaddiyar huldar ke tsakanin kasashen 2, wadda ta kara karfafa daga ranar 4 ga watan Oktoba, ranar da ‘yan ta’adda suka hallaka sojojin Nijar 5, da guda 4 na Amurka.
Matashiyar ‘yar majalisar wakilan Amurka ‘yar asalin kasar Somalia Ilhan Omar, na daga cikin mambobin wannan tawaga. Ta kuma nuna damuwa a game da rikice rikicen dake damun Afirka.
Ilhan Omar, tace zasu duba hanyoyin amfani da karfin soja don samarda tsaro cikin gaggawa, sannan zuwa gaba su dauki matakan bayarda tallafin da zai taimaka a tanadi hanyoyin samarda ci gaba mai dorewa ga al’umomi.
Bisa ga cewarta matakan da za a dauka sun hada da samar da kariya ga ‘yan mata, da ma magidantan dake fama da talauci don kaucewa fadawa tarkon ‘yan ta’adda na daga cikin batutuwan da tawagogin kasashen biyu suka tantauna akansu.
An yi wannan ganawar ne akan idon jakadan Amurka a Nijar Ambasada Eric Whitiker.
Ga cikakken rahoto daga wakilin Muryar Amurka Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum