A Jamhuriyar Nijar, ‘yan asalin yankin Diffa mazauna birnin Yamai sun bukaci gwamnatin kasar ta kara tsaurara matakan tsaro da nufin bai wa kamfanonin man fetur da ma jama’ar yankin damar gudanar da ayyukansu ba tare da wata fargaba ba.
Sun yi wannan kira ne da nufin ganin an farfadowar da tattalin arzikin yankin da ya durkushe yau shekaru kusan hudu, sanadiyar rikicin Boko Haram.
Daruruwan mutane maza da mata ‘yan asalin yankin Diffa mazaunan birnin Yamai ne suka hallara a taron da kungiyarsu ta kira a wunin jiya Lahadi da nufin tattaunawa akan mawuyacin halin da jama’ar Diffa ta tsinci kanta ciki.
Yankin na Diffa na da arzikin danyen mai amma kuma matasansa na fama da zaman kashe wando a sanadiyar rikicin Boko Haram.
Baya ga haka, noma, kiwo da kamun kifi na daga cikin ayyukan da jama’ar Diffa musamman na kewayen tafkin Chadi da kogin Komadougou ke dogara akansu domin hucewa kai takaici.
Sai dai rahotanni na nuni da cewa a ‘yan shekarun nan, kusan komai ya durkushe sakamakon tabarbarewar tsaro.
Garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da kisan fararen hular da ba su ji ba ba su gani ba da satar dukiyoyi ko fashi da makami na daga cikin matsalolin da suka yi dalilin kafa dokar ta baci a Diffa, matakin da ya kai ga rufe kasuwanni da dama.
A saurari cikakken rahoton wakilin Muryar Amurka Sule Mumuni Barma
Facebook Forum