Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC ta ce kashi saba’in cikin dari na matsalar zarmiyar kudi da almundahana a kasar, a bangaren hada-hadar banki ake aikata su. A kowacce shekara, dubban ‘yan Najeriya su na kai rahoton almundahana ga hukumomi.