TASKAR VOA: Bikin Ranar Samun 'Yancin Kan Najeriya Karo Na 64
A makon nan Najeriya ta yi bikin cika shekara 64 da samun ‘yan cin kai. A jawabinsa shugaban Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na samun nasarar yaki da ta’addanci da ‘yan fashin daji. Jawabin shugaban ya zo ne daidai lokacin da matasa a wasu sassan Najeriya suka gudanar da zanga-zangar matsin rayuwa