Wannan na zuwa ne biyo bayan samakon zabubbukan da galibi sai jam'iyya mai mulki ce kullum ke lashe kusan dukkan kujeru da aka yi takarar su.
Tsohon gwamnan jihar Gongola a jamhuriya ta biyu, Jakada Wilberforce Juta, ya ce kawo yanzu dimokaradiyya na tafiyar hawainiya sakamakon barin hakkin tafiyar da zaben a wuyan gwamnatocin jihohi da mafi yawan lokata basa kamanta adalci da gaskiya, dalilin da yasa masu kada kuri'a ke ‘kasa a gwiwa wajen fitowa zabe saboda akasin abin da suka zaba sakamakon zabe ke bayyanawa a jihohi.
Shi ma da yake sharhi kan zabubbukan kananan hukumomin da kuma tasirinsa ga makomar dimokaradiyyar Najeriya, tsohon kwamishinan hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta jihar Gombe, Barista Kashim Gaida, shawara ya bayar na idan ba za a yi wa dokar zaben garanbawul ba, to ya kamata a rika barin gwamnatocin jihohi suna daukar wadanda za su nada kwamishinonin zabe daga kowanne sashin kasar kamar yadda takwararta ta tarayya ke yi, ko ta kamanta gaskiya a harkar zaben kananan hukumomin.
A baya dai gwamnatin tsohon shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, ta shirya tarurrukan jin ra'ayoyi jama'a kan gyara dokar kundin tsarin zabe a shiyoyi shida, inda baki ya zo daya kan bukatar mikawa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa hakkin gudanar da zaben, amma majalisun tarayya suka yi fatali da shi domin dalilai na son rai.
Muryar Amurka ta yi kokarin jin ta bakin shugaban kwamitin yada labarai na majalisar wakilai Hon. Abdulrazak Namdas, kan ko me yake kawo cijewar gabatar da dokar? Amma hakka bai cimma ruwa ba.
Akwai alamu an fara samun sauyin tunanin wasu gwamnonin jihohi wadanda a baya ke ganin gabatar da dokar zata hana su anfana daga kudade da suke tatsa daga kaso da gwamnatin tarayya ke baiwa kananan hukumoin kamar yadda gwamnan jihar Taraba Arch. Darius Dickson, ya fada a hirarsu da wakilin Muryar Amurka, Sanusi Adamu, cewa ya gwammace gwamnatin tarayya ta dauki dawainiyar gudanar da zaben kananan hukumomin don su sami damar aiwatar wa jama'a ayukan rayawa.
Domin karin bayani ga rahotan Sanusi Adamu.
Facebook Forum