Jami’an kasar Iraq sunce tashin wasu bama bamai guda biyu a yau Alhamis wadanda kila an auna su ne akan jami’an yan sanda sun kashe mutane ashirin da bakwai da raunana mutane sittin da tara a kusa da hedikwatar yan sanda a birnin Kirkuk wanda ke arewacin kasar. Kamfanin dilancin labarun Associated Press ya ambaci wani jami’in yan sanda mai suna Sherzad Mofari yana fadin cewa, bam na farko ya tashi ne a wurin ajiye motoci na wani gini, sa’anan kuma sai wata mota dake kusa tayi bindiga yan mintoci kalilan bayan tashin bam na farko a yayinda yan sanda suke saurin zuwa wurin. Jami’ai sunce ba’a sa’a guda da aukuwar wannan al’amari ba sai aka raunana wasu jami’an tsaro takwas a wani al’amari. Yan sanda sunce wani bam ne ya tashi a kusa da jerin gwanon motocin yan sanda a birnin. Wannan ne karo na biyu a wannan watan da ake auna yan sanda wajen kai irin wadannan hare hare. Birnin Kirkuk yana kimamin tazarar kilomita maitan da hamsin arewa da Bagadaza baban birnin kasar ta Iraqi.
Jami’an kasar Iraq sunce tashin wasu bama bamai guda biyu a yau Alhamis wadanda kila an auna su ne akan jami’an yan sanda sun kashe mutane ashirin da bakwai da raunana mutane sittin da tara a kusa da hedikwatar yan sanda a birnin Kirkuk wanda ke arewacin kasar.
Labarai masu alaka
Nuwamba 09, 2024