Shugaba Barack Obama na Amurka yayi marhabin da sauye-sauye na ban mamaki dake faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya da Arewacin Afirka, amma kuma yace kasashe da yawa sun mayarda martani da tashin hankali ga kiraye-kirayen sauyi.
Shugaba Obama, wanda yake magana jiya alhamis a ma’aikatar harkokin waje, yace misali mafi muni na wannan shine kasar Libya, inda yace shugaba Muammar Gaddafi ya kaddamar da yaki a kan al’ummarsa. Yace idan da Amurka da kawayenta ba su dauki mataki ba, to da an kashe dubban mutane a Libya.Ya ce ita ma kasar Sham ta hau turbar kisa da kame-kame.
Mr. Obama yayi kira ga shugaba Bashar al-Assad na Sham da ya jagoranci sauyin dimokuradiyya ko kuma ya sauka daga kan mulki. A yayin da yake magana kan Masar da Tunisiya, Mr. Obama ya lura cewa a cikin watanni 6 da suak shige, shugabanni biyu sun kau daga kan mulki. Yace wasu kari na iya sauka a yayin da jama’arsu ke neman sauyi.
Yace Amurka ta samu wata dama mai dimbin tarihi ta tallafa musu, ya kuma ce zai zamo manufar Amurka ta fifita sauye-sauye a yankin tare da tallafawa shimfida dimokuradiyya. A halin da ake ciki, shugaba Barack Obama na Amurka ya bayyana goyon bayansa ga wata muhimmiyar bukatar Falasdinawa game da kafa kasarsu a nan gaba, yana mai fadin cewa bakin iyakar kasar Falasdinu, ya kamata ta zamo daidai da bakin iyakokin yankin kafin yakin kwanaki 6 na shekarar 1967, amma da sharadi.
A muhimmin jawabin da yayi kan manufofinsa game da yankin gabas ta tsakiya, Mr. Obama yace ya kamata bakin iyakar Isra’ila da Falasdinu ta kasance daidai da bakin iyakar sassan a shekarar 1967, amma sassan biyu su na iya musanyar yankuna ta yadda zasu samu bakin iyakar da suka amince da ita kuma mai tsaro.
Shugaban na Amurka yace tilas ne a ba Falasdinawa ikon mulkin kansu a kasa mai diyauci, wadda kuma ba ta rarrabe, watau babu wata kasar da ta raba Falasdinu gida biyu. Firayim ministan bani Isra’ila, Benjamin Netanyahu, yayi watsi da wannan furuci na Mr. Obama, yana mai fadin cewa Isra’ila ba zata iya kare kanta ba idan ta koma ga bakin iyakokin 1967.
Haka kuma yace idan Isra’ila ta janye zata bar wasu muhimman unguwannin yahudawa ‘yan share ka zauna a yankin yammacin kogin Jordan wadanda ba su cikin Isra’ila. Mr.
Obama zai karbi bakuncin Mr. Netanyahu yau jumma’a a fadarsa ta White House a wata ganawar da ake ganin zata zamo mai tankiya. Mr. Obama dai ya sha batawa da firayim ministan na nIsra’ila a kan batun Isra’ila da Falasdinawa a baya.