Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Tashar CNN Ta Kai Karar Fadar White House


Shalkwatar CNN a Atlanta.
Shalkwatar CNN a Atlanta.

Tashar labarai ta CNN ta yi karar gwamnatin Trump a Kotu a wani yunkurin maidowa babban wakilinta a fadar White House izinin daukar labarai a fadar da aka janye.

Sakatariyar labaran fadar White House Sarah Huckabee Sanders ta yi fatali da karar da CNN ta shigar, tana mai cewa gwamnatin tana kan bakarta na janye izinin daukar labaran da aka yiwa Jim Acosta.

Sanders ta fitar da sanarwa cewa, bayan Mr. Acosta ya yiwa shugaban kasa tambayoyi guda biyu kuma shugaban ya bashi amsa, sai yaki mika abin Magana na fadar White House domin sauran manema labarai su yi tambayoyinsu. Wannan ba shine karon farko da Acosta ya hana sauran manema labarai damar yin tambayoyi ba.

Da aka tambayi shugaba Donald Trump a wurin wani bukin White House a kan batun karar da CNN ta shigar a kotu, sai yace "zamu yi wannan Magana daga baya."

An shigar da kara ne a wata karamar kotun Washington kuma an mika batun ga alkali Timothy Kelly, wanda Trump ya nada atoni janar na kasar.

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG