A koda yaushe mahukunta na bayyana kokarinsu na inganta jindadin matasa bisa ga dukkan alamu matakin bazai samu nasara ba sai an hada kafi da karfe wajen daya tsakaini mahukuntan Turai dana Afirka da na sauran kasashen masu tasowa na yaki da azzaluman shuwagabani da ake zargi da wawushe dukiyar kasashen su zuwa kasashen ketare.
Wasu daga cikin matasan sun shedawa wakilin muryar amurka , Babangida Jibrin, cewa sun yi karatun boko har zuwa matakin digiri a fannoni daban daban amma zaman su a kasasshen su ba zai samar masu makoma mai kyau ba.
A can baya an kafa hukumomi domin kula da hana safarar mutane zuwa kasashen ketare.
Wasu matasa sun fadawa muryar Amurka cewa matukar abubuwa sun daidaita a Najeriya to tabbaci hakika babu inda zasu je suka ce har gori ake yi masu cewa me suke nema duk da arzikin da Allah ya yiwa Najeriya.