Taron da za'a yi a Austria shi ne zagaye na biyu na shawarwari kan rikicin da ake yi a Syria a sabon yunkuri na shara makomar kasar a siyasance, bayan zaman farko da suka yi a wajajen karshen watan Oktoba.
A jawabin bayan taron farkon,manyan kasashen duniya 17 ciki harda Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar tarayyar Turai sun amince kan bukatar gaggauta daukan matakan difilomasiyya domin kawo karshen rikicin da ake yi a Syria.
Hakan nan manyan kasashen sun amince da Majalisar Dinkin Duniya ta jagoranci shiri da zai kunshi shawarwari tsakanin gwamnatin Syria da kuma 'yan hamayya masu sassaucin ra'ayi, da zai kai ga tsagaita wuta.
Amma har yanzu akwai sabanin ra'ayi sosai kan wasu batutuwa, da suka hada da makomar shugaban kasar Bashar al-Assad.
A karshen zaman na farko sakataren harkokin wajen Amurka John kerry yace shi da takwarorinsa na Rasha da Iran da wasu jakadu sun amince cewa suna da sabanin ra'ayi kan rikcin da ake yi a Syria da kuma mafita.