Daya daga cikin zabin da Majalisar Dinkin Duniya take da ita shine tura sojoji daga makwabciyar kasar wato Kwango.
"kwamitin sulhu ya zauna cikin wannan mako domin daukan dukkan matakai da suka ga ya wajaba domin karin matsin lamba ga hukumomin kasar da suke Bujumbura, da gargadin kan hadari da ke tattare daukar munanan matakan da zasu yi illa ga jama'a masu yawan gaske," inji jakadan Britaniya Mathew Rycroft, jiya Laraba.
Haka nan kungiyar hada kan kasashen Afirka wato African Union ko AU tana iya tura sojojin kiyaye zaman lafiya zuwa Burundin.
Amma jami'an kasar suka ce ba "rikici ya rufe kasar baki daya ba," saboda haka babu yadda za'a yi a fada fitinar da zata kai ga kisan kiyashi.
Rikici da yake da nasaba da zabe ya halaka akalla mutane 240 ya kuma tilastawa dubban jama'a gudun hijira zuwa kasashen dake makwabta da kasar, tun bayan shugaban kasar Pierre Nuklurunziza ya ayyana ta zarce cikin watan Afrilu.
An zabensa cikin watan Yuli, zaben da 'yan hamayya suka kaurace ma kuma suka kira matakin da shugaban kasar ya dauka a zaman wandya sabawa tsarin mulkin kasar.