WASHINGTON, DC —
A kokarin kawo zaman lafiya tsakanin makiyaya da manoma a jihar Oyo wata karamar hukuma ta shirya taron kawo fahimtar juna.
Karamar hukumar Orire ta shirya taron tattaunawa tsakanin makiyaya da manoma na yini daya.An yi taron karkashin wani jami'in karamar hukkumar Alhaji Bayo Raji. Yace ya kamata a tattauna tsakanin bangarorin biyu domin a shawo kan duk wani rikici da ya taso. Shi ma shugaban karamar hukumar Chief Jacob Bamigboye yace kowa ya zauna lafiya da juna tunda dukanmu 'yan Najeriya ne. Ya shawarci makiyayan su tabbatar cewa idan shanu nada yawa to a sa mutane da yawa su bisu.Misali ba daidai ba ne a sa yaro dan shekara goma ya bi shanu dari. Yace dole ne su yi barna domin yaron ba zai iya shawo kansu ba haka mutum daya bai isa shanu dari ba.
Da ya juya kan manoma sai ya rokesu su daina sa sinadarai masu guba dake kashe shanu. Wani manomi yana ganin idan aka kafa kwamiti da ya kunshi manoma da makiyaya zai taimaka kwarai. Shi kuma makiyayi Alhaji Sani yace idan sun koma gida zasu tara makiyaya su yi masu gargadi.
Taron ya samu halarta 'yansanda da 'yansandan ciki wato SSS da jam'an farar hula ko Civil Defence da dai wasu makamantansu.