Dubnu dubatar Musulmai daga kasashen Afirka bakwai na kungiyar tattalin arzikin Afirka suka taru a Lagos domin halartar wa'azi da kungiyar Izalatul Bidi'a Wa'ikamatul Sunna ko, Izala a takaice, ta shirya.
Yayin da yake magana da manema labarai kafin a fara taron shugaban kungiyar a Najeriya Sheikh Abdullahi Bala Lau yace hanya daya da za'a iya samun zaman lafiya a Najeriya shi ne idan shugabannin addini suna fadawa masu rike da madafin iko gaskiya. Yin hakan shi ne kadai yadda za'a samu dawamammen zaman lafiya tsakanin mabiya addinan nan biyu da suka yi tasiri a Najeriya. Ya ce duka addinan biyu sun koya wa mabiyansu yadda zasu zauna da abokan zamansa da ba addininsu guda ba.
Sheikh Bala Lau yace "Idan malaman addinan duka guda biyu zasu bi karantarwar da addininsu yayi umurni to za'a samu cikakken zaman lafiya. Kowa akwai yadda addininsa ya fada ya yi muamala da abokin zamansa. In zai bi irin wannan to za'a zauna lafiya...Kuma wadanda suke da madafin iko a yi kokari ana yi masu wa'azi da karantarwa su ji tsoron Allah su jagoranci al'umma da adalci"
Da wakilin Muryar Amurka ya ce ma Shekh Bala Lau cewa duk da wa'azin da suke yi a masallatai da yawa da mijami'u amma ayyukan asha sai dada karuwa su keyi, sai yace "In ka samu mutum dubu daya dari tara da casa'in da tara kusan rabon Shaidan ne. Daya ne kawai ake samu na Allah. Don haka wannan ba zai sa a daina wa'azi ba kuma Allah Ya nuna a Kur'ani cewa idan ba'a wa'azi da karantaswa to Ya kan kawar da kansa da barin al'umma. Al'umma zata shiga cikin wahala. Don haka har yanzu ana samun wadanda suke gyarawa suna tsoron Allah domin wa'azi zuciya yake gyarawa na dan adam"
Wannan shi ne karon farko da kungiyar ta shirya yi wa'azi a Lagos. Sheikh Bala ya ce sun lura cewa akwai kungiyoyin musulmai a kudancin kasar dake yin wa'azi irin nasu shi ya sa suka ga yakamata su zo Lagos. Ban da haka ma ya ce makasudinsu shi ne su kawo hadin kai da musulmai da ma ba wadanda ba musulmai ba. Domin ma samun hadin kai da musulmai da kirista ya sa aka kafa wani kwamiti dake karkashin Sarkin Musulmi dake tattaunawa tsakanin addinan biyu lokaci lokaci. Yace kungiyar na iyakacin kokarinta na kawo fahimta tsakanin addinan biyu, Yace da Allah na son addini guda kawai da ya yi hakan.