Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taliban Ta Yi Biris Da Gwamnatin Afghanistan


Wakilan kungiyar Taliban yayin da suka isa wajen tattaunawa a birnin Doha na kasar Qatar, ranar 29 ga watan Fabrairu, 2020.
Wakilan kungiyar Taliban yayin da suka isa wajen tattaunawa a birnin Doha na kasar Qatar, ranar 29 ga watan Fabrairu, 2020.

Kungiyar Taliban mai ta da kayar baya, ta ki amincewa da tayin zaman sulhu da wani kwamitin gwamnatin Afghanistan ta kafa ya yi mata.

A cewar kungiyar, yin hakan zai saba yarjejeniyar zaman lafiya da suka kulla da Amurka.

Matakin kin amincewa da wannan ta yi na zuwa ne kwana guda bayan da mayakan Taliban suka kai wasu hare-hare akan dakarun Afghanistan a arewacin kasar.

Hare-haren sun ba su damar karbe ikon wata gunduma da ke yankin.

A ranar Alhamis, Shugaba Ashraf Ghani ya ayyana kafa kwamitin mai mambobi 21 domin tattaunawa da yadda za a raba mukamai da kungiyar ta Taliban

Wakilin Amurka na musamman Zalmay Khalilzad wanda ya shiga tsakani aka kulla yarjejeniya da Taliban a ranar 29 ga watan Fabrairu, ya yaba da kafa kwamitin, matakin da ya ce ya kara sharar fage ga shirin zaman sulhu na cikin gida.

Sai dai a ranar Asabar, kakakin kungiyar ta Taliban, Zabihullah Mujahid ya yi watsi da kwamitin yana mai cewa bai Samu wakilcin dukkanin al’umomin kasar ba.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG