Mayakan Taliban sun dauki alhakin kai wani hari da aka kai a sansanin sojin Afghanistan da matattarar bayanan sirri dake lardin Helmand a daren jiya Lahadi, wanda yayi sanadiyar mutuwar mutum 7 tare da raunata fiye da dozin, a cewar wata majiyar tsaro.
Jami’an Afghan sun tabbatar da kai harin, wanda ya hada da mai Magana da yawun gwamnan Helmand Omar Zawak, wanda ya ce wadanda suka jikkata basu da yawa. Ma’aikatar tsaron Afghanistan ta ce mutun daya ne ya samu rauni.
Majiyar da ta bukaci da a sakaya suna, ta ce wani sanssanin dake lardin Grishk shima an dai-daita shi.
Kwamishinan ‘yan Sanda na yankin Ismail Khpalwak, ya ce wani dan kunar bakin wake ne ya tada wata mota kirar Mazda a bakin kofar shiga wajen. Sansanin dake kan hanyar zuwa Kandahar na da tazarar kilomita 120 da yankin arewacin birnin Lashkargah, inda jami’an tsaro masu lura da babbar hanyar ke zaune.
A wata sanarwa da Kungiyar Taliban ta fitar na daukar alhakin harin, ta ce na ramuwar gaya ne, saboda ci gaba da sabawa yarjejeniyar da aka cinmma da Amurka da kungiyar ta Taliban a watan Fabrairu a Doha, kana da kai hari ga fararen hula a yankunan da Taliban ke rike da ikon su.
Facebook Forum