Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kullen Korona: An Bar Mutane Su Dan Fita Shan Iska a Kasar Spain


Wasu 'yan Spain kalilan na shan iska a gabar ruwa
Wasu 'yan Spain kalilan na shan iska a gabar ruwa

A karon farko cikin makwanni bakwai, gwamnati ta bar mutanen kasar Spain su dan fito shan iska jiya Asabar, wanda don haka miliyoyin mutane su ka basu kan tituna saboda fara sassauta matakan takaita zirga-zigar da ta dauka don dakile yaduwar cutar korona.

Masu guje gujen motsa jiki, da mahaya kekune da masu lailayar bisa teku su ka fantsamo waje tun da wuri su ka riga ‘yan shekaru 70 fita na tsawon sa’o’i hudu, kafin su kuma aka barsu su dan leko waje na tsawon sa’o’i biyu, su kuma yara ‘yan kasa da shekaru 14 aka barsu su fito daga karfe 12 na rana zuwa 7 na almuru.

“Mu na moran ladar sadaukar da kai da mu ka yi ne na makwannin nan masu tsawo,” a cewar Firaministan Spain Pedro Sanchez.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG