Koriya Ta Arewa ta kaddamar da hari da bindgogin artilari kan wani tsibirin Korita Ta Kudu dake kan iyaka,wanda ya janyo martani nan da nan daga mayakan Koriya Ta Kudu, kuma suka zaburadda jiragen yakinsu cikin gaggawa.
Rundunar mayakan Koriya Ta Kudu tace an kashe sojoji biyu, 12 kuma suka jikkata a lamari irinsa mafi muni tsakanin sassan biyu,bayan gwabza yakin Koriya da sassan suka yi.
Rahotani daga kafofin yada labarai sunce wuta ta kama gidaje masu yawa,an kuma jikkata farar hula biyu. Hukumomin Koriya Ta Kudu sun kwashe fiyeda farar hula dubu daya dake tsibirin na Yeonpyeong, zuwa wasu sansanonin ko ta kwana.
Shugaba Lee Myung-bak ya kira taron gaggawa na ministocin tsaro, jami’ai suka ce yana kokarin hana musayar harbe harben daga kazancewa. Duk da hak gwamnatinsa ta yi gargadin mummunar martani idan aka sake kawo mata hari.