Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Coronavirus Na Da Sauran Lokaci a Duniya - WHO


Shugaban WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus
Shugaban WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus

Jiya Litinin Shugaban Hukumar Lafiya ta Duniya WHO, ya yi gargadin cewa annobar cutar coronavirus ba ta ko kusan zuwa karshe ba, duk kuwa da cewa wasu kasashe sun fara sassauta matakan kariyarsu.

“Ku yarda damu. Har yanzu ba mu ga mafi munin wannan bala'in ba,” abin da shugaban WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ya fada kenan, ya ci gaba da cewa “Bari mu tare wannan bala’in. Cuta ce da mutane da dama ba su fahimce ta ba."

Ya kwatanta cutar coronavirus, wadda a fadin duniya ta kama mutane kusan 2.5, ta kuma kashe mutum sama da 167,000; da cutar murar Spanish flu ta alif 918, wadda ta kashe mutane har miliyan 100. Amma ya ce, irin wannan makoma ba dole bane sai ta faru ba.

“Yanzu muna da fasaha, zamu iya kau da bala’in, zamu iya kare kanmu daga shiga irin wannan tashin hankalin,” a cewar Tedros.

Yawancin kasashe sun sassauta matakan da aka dauka kan coronavirus jiya Litinin.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG