Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Takaddama Kan Cire Tallafin Man Fetur a Najeriya


Takaddama ta kunno kai tsakanin kungiyar kwadago da kungiyar gwamnonin Najeriya kan cire tallafin Man fetur.

Tun farko dai kungiyar gwamnoni na ganin ya kamata a kara kudin Man fetur zuwa Naira 385, ya yin da kungiyar kwadago ta ce ba za ta lamunta ba wanda hakan ya sa ta aikawa gwamnati takardar gargadi.

Yanzu haka dai kungiyar kwadago ta ce ta aikawa da mahukuntan kasar da wasikar dake dauke da bayanai da kuma kira da gwamnonni su ka yi cewa ana iya kara kudin Man fetur daga Naira 162 zuwa 385, don a hana fara kwaurin Man.

Sakataren tsare-tsare na kungiyar kwadago, Kwamrad Nasiru Kabir, ya yiwa sashen Hausa karin haske akan wasikar da kungiyar kwadago ta rubuta ga kungiyar gwamnonin Najeriya, tare da tambayar ko tallafin da ake cewa ana cirewa kullum yana haihuwa?

Kwarad Nasiru, ya kara da cewa kasancewar talakawa ne ke shan wahala don haka kungiyar kwadago tana bayan talakawa akan duk wani abin da zai kawo musu saukin rayuwa don haka karin kudin Man fetur batu ne da ba za a lamunta ba.

To sai dai a daidai lokacin da hakan ke faruwa, shugaban kungiyar masu masana’antu ta kasa MAN, Segun Ajayi Kadiri, ya yi hasashen cewa danyen Man fetur ya kara kudi a kasuwannin duniya, saboda haka ya zama wajibi farashin Mai ya sauya ko za a cire tallafi ko akasin haka.

Amma, shugaban ma'aikatar Man fetur ta kasa Mele Kolo Kyari, ya ce cire tallafin shi ne kadai abin da zai taimaka wa kasa domin gwamnati ta dade ta na kashe makudan kudade, amma talakawa ba sa gani a kasa.

Shi kuwa tsohon shugaban kungiyar ma’aikatan Man fetur ta kasa, Kwamrad Isa Tijjani, na ganin gyara matatun Man kasar ne kadai zai taimaka, idan har gwamnati ta dauki nauyin ganin an yi gyaran cikin sauki kuma kan lokaci. Saboda a samarwa talakawa sauki a fannin sufuri wanda shine ginshikin rayuwar talaka.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Medina Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:49 0:00


XS
SM
MD
LG