Yayin da ake ci gaba da tada jijiyar wuya tsakanin Turkiyya da Amurka kan sayan makami mai linzami daga Rasha, Gwamantin Turkiyya na neman karkata ga kungiyar tsaro ta NATO mai sassaucin ra'ayi kan wannan takaddama ta sayan makamai.
Mataimakin shugaban kasar Amurka, Mike Pence, ya yi gargadi a wannan watan cewa makomar Turkiyya a kungiyar tsaro ta NATO tana cikin hatsari idan gwamnatin Turkiyya ta yarda ta karbi S-400, makami mai linzami na Rasha, abinda ya janyo maida martani cikin fushi daga mai magana da yawun shugaban Turkiyya Ibrahim Kalin.
Gwamnatin Amurka ta yi ikirarin makamin mai linzami na S-400, wanda wa’adin da za a mikashi shine watan Yuli, yana barazana ga tsaro da tsarin sojojin kungiyar tsaro ta NATO a Turkiyya, musamman ma, sabon jirgin yakin samfurin F-35. Rasha tana ci gaba da kera S-400 don yin gogayya da fasahar F-35.
Facebook Forum