Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Taho-Mu-Gamar Jiragen Ruwan Amurka Da China


Kimanin mitoci kadan suka rage tsakanin jirgin ruwan Amurka da na China su yi karon batta, a kan tekun yankin Kudancin China.

Wata-taho-mu gamar da ta kusa aukuwa tsakanin jiragen ruwan China da Amurka akan tekun kudancin China da ake takaddama akai, ta girgiza kasashen Asiya.

Jirgin Amurkan ya kusanci na China da kimanin mitoci 40 a tekun kudancin china, a ranar 30 ga watan Satumba, wanda ya yi sanadiyar jirgin Amurka ya canza hanya shi, a cewar ma’aikatar Pentagon.

China na ikirarin cewar kashi 90 na tekun ita ke iko da shi, amma Amurka ta ce sauran kasashe ma na da hakki akai.

A ranar Asabar shugaban tsaro daga tawagar mutane 10 na kungiyar jiragen ruwa na kudancin Asiya, ba su amince da wannan matakin ba, hakan ya sa suka bukaci a yi wani taro a Singapore don bayyanar da hakkin kowa, da kuma sanin hurumin China daga Amurka.

Kasashen dai sun nuna damuwarsu, don hatsarin ka iya faruwa nan gaba, da kuma tsoron haramta amfani da tekun da Amurka ke kokarin yi.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG