Kamar yadda Taliban din suka bayyana a wata sanarwa da suka bayar cikin harshensu na Pashto.Sun fadi cewa har yanzu shugabanninsu ba su yanke shawarar shiga tattaunawar ba.
Inda suka kara da cewa, tattaunawar ba zata iya haifar da da mai ido ba sai in har dakarun kasashen waje sun fice daga Afghanistan. Tare da cire takunkuman da aka sa akan shugabanin tawayen Taliban.
A kuma sakin dukkan fursunoninsu da ake tsare da su. Sanarwa ta ci gaba da cewa, an kara kai sojin Amurka zuwa filin daga wanda hakan ya karawa sojin Afghanistan karfin kai hare-hare.
A nan birnin Washington kuma, Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta yi kira ga ‘yan Taliba din da su canza shawara don komawa kan teburin sulhun da zai zamewa dukkan sassan biyu maslaha.