Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ta Yiwu Wani Rigakafin Cutar AIDS Ya Kawo Karshen Cutar


Wani sabon maganin HIV
Wani sabon maganin HIV

Kamfanin sarrafa magungunan Gilead zai ba da izinin sayar da irin maganin kariyar cutar HIV da ya sarrafa mai rahusa a kasashe masu tasowa inda cutar HIV at fi yaduwa, ciki har da kasashen Afrika.

Rigakafin cutar AIDS da ake yi sau 2 a shekara yana aiki 100 bisa 100 wajen hana kamuwa da cutar SIDA mai karya garkuwar jiki a cewar wani bincike da aka yi kan mata, kuma sakamakon binciken da aka wallafa a ranar Laraba ya nuna cewa, yana aiki a maza.

Kamfanin magungunan Gilead ya ce zai ba da izinin a sayar da irin maganin mai rahusa a kasashe marasa karfi guda 120 da ke da masu kamuwa da cutar SIDA da yawa, galibinsu a Afirka, Kudu maso Gabashin Asiya da yankin Karebiya. Amma ya ware kusan dukkanin kasashen yankin Latin na Amurka, inda adadin masu kamuwa da cutar bai da yawa amma yana karuwa, lamarin da ke kawo damuwa kan cewa kasashen duniya na rasa wata muhimmiyar dama ta dakile cutar.

"Ya zuwa yanzu wannan maganin shi ya fi duk wani rigakafi da muke da shi, wanda ba a taba ganin irinsa ba," a cewar Winnie Byanyima, babbar darektar hukumar UNAIDS. Ta yaba wa kamfanin Gilead don hada maganin amma ta ce damar kasashen duniya ta dakatar da yaduwar cutar SIDA ta dogara ne akan amfani da rigakafin a kasashen da ke da hadarin cutar sosai.

A cikin wani rahoto da aka fitar don bikin ranar cutar AIDS ta duniya a ranar Lahadi, hukumar UNAIDS ta ce adadin wadanda suka mutu sanadiyar cutar a bara, da yawansu ya kai kimanin 630,000, shi ne adadi mafi kankanta da aka gani tun bayan lokacin da cutar ta yi kamari a shekarar 2004, abin da ke nuni da cewa, a yanzu kasashen duniya na a matakin da zasu iya daukar matakan kawo karshen cutar ta.

An riga an fara sayar da maganin da ake kira lenacapavir a karkashin sunan Sunlenca don jinyar cututtukan HIV masu karya garkuwar jiki a Amurka, Canada, Turai da sauran wurare. Kamfanin yana shirin neman izini nan ba da jimawa ba don amfani da Sunlenca a matsayin rigakafin cutar HIV. Duk da cewa akwai wasu hanyoyin kariya daga cutar, kamar kwaroron roba, magungunan da ake hadiya kullum, da alurar da ake yi sau 2 a wata, masana sun ce alurar rigakafin kamfanin Gilead da ake yi sau 2 a shekara zai kasance da muhimmanci musamman ga mutanen da ke fuskantar wariya da yawancin lokuta ke jin tsoron neman taimako, ciki har da ‘yan luwadi, masu sana’ar karuwanci da mata matasa.

"Zai kasance wani abin al'ajabi ga wadannan rukunonin mutanen, saboda hakan na nufin zasu je asibitin karbar rigakafin sau 2 a shekara," in ji Byanyima ta hukumar UNAIDS.

A cikin wata sanarwa, kamfanin Gilead ya ce yana da kudurin taimaka wa wajen ba da damar samun rigakafin cutar HIV inda ake matukar bukata. A cikin kasashen 120 da suka cancanci samun irin rigakafin na kamfanin akwai 18 da galibi daga kasashen Afrika ne, wadanda ke da kashi 70 cikin 100 na adadin masu cutar HIV a duniya.

Kamfanin sarrafa magungunan ya ce ya na kuma aiki don ganin an samu hanya mafi sauki mai aiki da maganin lenacapavir zai isa ga mabukata don kariyar cutar HIV.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG