Hukumar yaki da cuta mai karya garkuwar jiki ta Najeriya NACA tace kudin da gwamnatin kasar ke amfani da su wajen sayen magungunan rigakafin cutar HIV/Aids ya karu daga naira 12, 666 a shekarar 2019 zuwa 377,000 a shekarar 2021.
Shugaban hukumar ta NACA Gambo Aliyu ne ya bayyana haka a lokacin gabatar da ayukan yaki da cutar a Najeriya daga shekarar 2007 zuwa 2022.
Shugaban hukumar yace an tattara kudin tallafin na yaki da cutar sida daga shekarar 2015 zuwa 2021 har dala biliyan 2.73 daga kungiyar tallafin agajin cutar ta gwamnatin Amurka (PEPFAR), yayin da tallafin da asusun duniya ya bayar ya kai dala miliyan 591.
Ya kara da cewa sauran nasarorin da aka samu daga shekarar 2015 zuwa 2021 sun hada da bunkasa rukunin jinya, manyan tsare-tsare da daidaita shirye-shiryen da za su amfani jama’a da sauransu, wanda hakan ya sa kasar ke dab da cimma tsare-tsaren hukumar UNAID na shawo kan cutar.
Aliyu ya ce hukumar na sa ran samun nasarar gudanar da rigakafin cutar daga uwa zuwa yaro, da kuma daukar matakan ganin cewa babu wani yaro da aka haifa da cutar a Najeriya.
Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha ya ce akwai bukatar hadin gwiwa da gwamnatocin jihohi wajen inganta tsari mai dorewa na samun nasara a yaki da cutar mai karya garkuwar jiki a Najeriya.