Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Kaddamar Da Aikin Ruwa A Zariya


Shugaba Muhammadu Buhari
Shugaba Muhammadu Buhari

Shugaba Buhari ya kai ziyara fadar Mai Martaba Sarkin Zazzau, yayin ziyarar aiki da kuma godiya ga al’ummar jahar Kaduna game da kuru’un da suka ba shi a karo na biyu.

A lokacin da shugaba Najeriya, Muhammadu Buhari, yake maida jawabi kan bukatar taimakawa jahar Kaduna, ya ce a rabon ministoci ya biya Kaduna da Kano saboda ya ba su manyan ministoci guda biyu-biyu.

Shugaban kasar ya sake nanata kokarin gwamnatinsa kan tsaro da bunkasa tattalin arziki, inda ya buga misali da yadda dumbin matasa da ke son gwamnati ta sama musu aiki, duk kuwa da yake wasu ba su da ilimin zamani wanda ya ce akwai bukatar arinka lakantar kundin tsarin mulkin kasa don sanin abun da gwamnatin tarayya da jahohi da kuma kananan hukumomi za su yi, ba komai aka kinkimo sai an danganta ga shugaban kasa ba.

Kaddamar da ruwan Zaria daya ne daga cikin manyan dalilan zuwan shugaba Buhari Kaduna, kuma Gwamna Nasiru Ahmed El-Rufai, ya ce da yawan mutanen da ba su wuce shekara talatin ba basu taba ganin ruwan fanfo a Zariya ba.

Gwamna El-Rufa’i ya kara da ce gudunmawar shugaban kasa da gwamnatin jihar Kaduna karkashin jam'iyyar APC yanzu an karya kwarin rashin ruwa a Zariya, wannan shi ya sa gwamnati ta ga ya dace ta gayyaci shugaban kasa don ya kaddamar da wannan aiki.

Tun farko sai da mai-martaba sarkin Zazzau, Alhaji Shehu Idris, ya yabawa Shugaban kasa sannan ya mika bukatun jahar Kaduna.

Sarkin ya ce ina rokon mai girma shugaban kasa da ya duba durkushewar masana'antu da gyara hanyoyin Zaria zuwa Pambegwa da Kaduna zuwa Jos da kuma Zariya zuwa Funtua.

Sannan ya ce duk da dadewar asibitin koyarwa na Zaria yanzu rashin kudi da sauran matsaloli sun hana aiki yadda ya kamata a saboda haka ya ce akwai bukatar shugaban kasa ya kawo dauki.

Saurari cikakken rahoton Isah Lawal Ikara daga Kaduna:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

Facebook Forum

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG