Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sulhu Ko Afuwa Ga ‘Yan Ta’adda Ba Zai Yi Tasiri Ba - Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya


Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya, Manjo Janaral Taoreed Abiodun Lagbaja
Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya, Manjo Janaral Taoreed Abiodun Lagbaja

Babban Hafsan hafsoshin sojojin Najeriya, Manjo Janaral Taoreed Abiodun Lagbaja ya bayyana cewa yin ahuwa ko yafiya ba shi da wani tasiri a yaki da ta'addanci ko shawo kan matsalar tsaro a Najeriya.

ABUJA, NIGERIA - Babban Hafsan sojin yace, 'yan bindiga ba zanen goyo bane, kasancewa yin sulhu ko afuwa ba abinda ya ke tsinanawa sai kara basu damar kara karfi su sake tattaruwa domin shirya sake ci gaba da kaddamar da hare-hare.

Bisa wannan matsayar Janaral Lagbaja ya umarci Babban Hafsa mai kula da kai hare-hare ya tsara yadda za a tunkari matsalar rashin tsaro a jihar zamfara.

Janaral Lagbaja wanda ke magana lokacin da Gwamnan jihar Zamfara Dr. Dauda Lawal Dare ya ziyarce shi domin kai koken irin yadda ‘yan bindiga ke cin karensu babu babbaka, ya ce duk wata matsala da ta shafi Zamfara, to zama Illa a jihohin Kaduna, Kebbi, Katsina da Niger.

Dauda Lawal Gwamnan Jihar Zamfara
Dauda Lawal Gwamnan Jihar Zamfara

Bisa wannan dalilin ya ce za a shirya kaddamar da farmakin bai daya lokaci guda tsakanin dakarun runduna ta daya dake Kaduna da kuma mayakan runduna ta takwas da ke Sokoto ta yadda in an afkawa ‘yan bindigan daga Kudu ba za su sami damar tserewa zuwa Arewa ba, ko in an afka masu daga Arewa ba za su samu damar tserewa zuwa Kudu ba.

Babban Hafsan Hafsoshin na Najeriya ya bayyana cewa abubuwa da dama ne suka assasa kalubalen tsaro a jihar Zamfara, kamar rigimar Makiyaya da Manoma, rikicin ‘Kabilanci da matsalar da ke da alaka da hakar ma'adinai, banda haka kuma, dukan bangarorin na rike da makamai.

Ya ce don tunkarar wannan matsala dakarun za su dauki kwakkwaran matakin yiwa tufkar hanci inda ya kara nuna lalle batun sullhu ko afuwa ga ‘yan ta'adda ba zai yi wani tasiri ba.

Wasu yan bindiga da aka kama
Wasu yan bindiga da aka kama

Galibin Zamfarawa sun gamsu da matsayar Babban Hafsan, kamar yadda wani mai fafutukar neman zaman lafiya a jihar ta Zamfara, Ibrahim Janyau ya bayyana a hirar shi da Muryar Amurka.

Ibrahim Janyau ya ce gwamnatocin Abdul'azeez Yari da ta Bello Matawalle duk sun yi irin wannan sasantawa amma kwalliya bata biya kudin sabulu ba.

Ya ce a baya-bayan nan lokacin da tsohon gwamnan jihar, Yariman Bakura ya kara tado da maganar afuwan ‘yan bindiga, sai suka kara zafafa kai hare-hare don dai a nemesu a tattauna dasu.

Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina:

Sulhu Ko Afuwa Ga ‘Yan Ta’adda Ba Zai Yi Tasiri Ba - Babban Hafsan Hafsoshin Najeriya.mp3
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG