Wannan dai shine karo na uku da Majalisar Dattawan Najeriya ke gayyatar sufeton ‘yan sandan Najeriya, domin ya bayyana gaban Majalisar ya yi bayani kan kashe-kashen dake faruwa a wasu jihohin kasar.
Haka kuma ana tsammanin zai yiwa ‘yan Majalisar bayani kan zargin cin zarafin da ‘yan sanda su ka yiwa ‘dan Majilsa Dino Melaye, wanda ya shafe makonni biyu a hannunsu.
Bayan yin shiru na wajen mintina goma a zauren Majalisa ana jiran shigowar Ibrahim Idris, sai shugaban Majalisar Bukola Saraki ya sanar da cewa sufeto din bai zo ba. kuma babu wani wakilinsa da ya aika.
Yanzu haka dai ana jiran ganin wanne mataki da kundin tsarin mulkin kasa Majalisar za ta dauka domin hukunta sufeton ‘yan sandan, bisa laifin yin watsi da umarnin ta.
Facebook Forum