Malami kuma attajiri Khalifa Isyaku Rabiu ya rasu ne a wani asibiti a Birnin London a kasar Birtaniya.
Jama’a sun soma yin tururuwa zuwa gidan marigayin dake Goron Dutse a cikin brinin Kano domin yiwa juna ta’aziya.
Wazirin Kano murabus Shaikh Nasiru Muhammad Nasir na cikin sahiban Khalifa Isyaka Rabiu. Ya ce sun rayu tare sun kuma taso tare kuma a wurin malami daya suka yi karatu kafin Allah ya karbi ransa bayan sallar magariba jiya. Ya bayyana shi Khalifa Isyaku a matsayin wanda ya haddace Kur’ani yana karantashi a gida, akan hanya da ma ofishinsa kana kuma gashi attajiri, mai son mutane da yawan yin kyauta.
Shi kuawa alaramma Malam Dauda Loko Makera a cewarsa rashi ne ga dukannin mahaddacin Kur’ani da dukannin wadanda suke yiwa Kur’ani hidima da duka masu son su koyi Kur’ani. Ya ce rashi ne a garesu ga baki daya.
A cikin wata sanarwa da kwamishanan labaran jihar Kano Muhammad Garba y araba a daren jiya gwamnatin jihar ta bayyana rasuwa attajirin kuma shaikh a matsayin asara ga muslman duniya gaba daya.
Ana sa ran za’a yi jana’izarsa gobe Alhamis bayan an kawo gawarsa daga Birtaniya.
Ga rahoton Mahmud Ibrahim Kwari da karin bayani