Haka kuma wannan sabuwar kasa ta duniya na huskantar kalubalolin kayan agaji, a yayin da dubban yan kasar suka gudu, suka yi hijira zuwa kasashen dake makwaptaka da ita don neman mafaka.
Deng ya fada jiya Alhamis a wurin taron MDD a New York, cewa halin da al’ummar kasar ke ciki na wahala ya wuce gona da iri.
Mataimakin shugaban na Sudan ta Kudu Deng ya kara da cewar yake-yake a wannan shekara a yankunan Wau, da Raja, da kuma Juba sun kara dagula al’amura.
Sai dai kuma ya dora laifi a kan ambaliyar da aka samu sakamakon ruwan sama kamar da bakin kwarya wadda ta fid da mutane daga gidajensu a jihohin Upper Nile da kuma Bahr al Ghazal.
Duk da wannan hali da ake ciki, Deng yace hankali ya soma kwantawa a kasar ta Sudan ta Kudu.
An dai yi wani zaman tattaunawa a jiya Alhamis a wurin taron MDD a kan rikicin Suda ta Kudu da kuma kalubalolin da take fuskanta na kayan agaji.