Gwamnan jihar Nasarawa Alhaji Umaru Tanko Al-Makura yace gwamnatinsa ta dukufa ne wajen tattaunawa da talakawa tsantsa, wato wadanda basu da wani mukami da kuma ba'a daukesu wani abu ba domin samar da zaman lafiya.
Gwamnan yace duk da matsalolin da suka fuskanta a can baya sun samu al'ummarus sun yi masu bayani. Yace sun amince da bayanansu kuma sun yadda. Yace akwai amana tsakanin gwamnatinsa da al'ummar jihar. Yace suna yin abu ne da mutanen da ake renawa saboda basu da wani mukami, ko ba'a daukesu komi ba, ko kuma suna da nakasa. Yace a wurinsu irin wadannan mutanen ne masu komi, su ne kuma masu mahimmanci a wurin gwamnatinsa.
Gwamnan ya cigaba da cewa idan za'a nemi zaman lafiya dasu za'a soma domin dasu za'a samu zaman lafiya. Yace sun samu zaman lafiya domin suna hulda da mutanen da basu da wani mukami. Su ne suka rike amana suna son a zauna lafiya.
Yace a halin da ake ciki yanzu tsaro da zaman lafiya ba a hannun soja ko dansanda suke ba hatta talakawa suna da na yi akan samarda zaman lafiya.
Muryar Amurka ta zanta da wasu shugabannin al'umma wadanda suka bukaci gwamnati da ta ajiye jami'an tsaro a yankunansu. Kodayake gwamnan jihar ya taimaka da kayan gini da abinci domin wadanda rikicin baya ya rutsa dasu mutanen Asakyo sun ki komawa saboda kabilar Eggon. Su ma 'yan kungiyar Fulani makiyaya sun gamsu da dawowar zaman lafiya.
Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.